Alhamis 23 Yuli 2026 - 21:43
An Gudanar da Majalisin Juyayin Shahadar Imam Hassan (A.S.) a Da'irar Bauchi

Hauza/ A daidai lokacin da ake tunawa da ranar shahadar Imam Hasan al-Mujtaba (A.S.) a ranar 7 ga watan Safar, mabiya Ahlul Baiti (A.S.) a Da'irar Bauchi ta Najeriya sun gudanar da majalisar juyayin wannan babban lamari domin tunawa da rayuwa da kuma irin sadaukarwar Jikan Manzon Allah (S.A.W.A).

Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya ruwaito cewa, almajiran Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) da ke Da'irar Bauchi sun gudanar da ranar farko ta majalisar juyayin shahadar Imam Hasan al-Mujtaba (A.S.) a ranar Laraba, 7 ga Safar 1448 Hijira, wadda ta yi daidai da 22 ga Yuli, 2026, a Husainiyyar da ke Unguwar Tafawa Balewa, Jihar Bauchi.

Majalisin ya samu halartar dimbin mabiya Ahlul Baiti (A.S.) da masoya Imam Hasan (A.S.), kuma an sanar da cewa za a kammala zaman a ranar Alhamis, 8 ga Safar, in sha Allah.

A ranar farko ta majalisin, Malam Abdullahi Ashura ne ya gabatar da jawabi, inda ya yi cikakken bayani kan rayuwar Imam Hassan (A.S.), matsayinsa mai girma, kyawawan ɗabi'unsa da kuma irin gwagwarmayar da ya yi wajen kare addinin Musulunci da isar da saƙon Allah da na ManzonSa (S.A.W.A).

Har ila yau, ya bayyana muhimman darussa da za a koya daga rayuwar Imam Hasan (A.S.), tare da jaddada muhimmancin yin koyi da ɗabi'unsa, haƙurinsa, hikimarsa da kuma tsayuwarsa kan gaskiya duk da ƙalubale da fitintinun da ya fuskanta a zamaninsa.

An kammala zaman ranar farko da addu'a da zaman makoki, yayin da masu shirya taron suka sanar da cewa za a ci gaba da gudanar da shirye-shiryen zaman a rana ta biyu, in sha Allah.

An Gudanar da Majalisin Juyayin Shahadar Imam Hassan (A.S.) a Da'irar Bauchi

An Gudanar da Majalisin Juyayin Shahadar Imam Hassan (A.S.) a Da'irar Bauchi

An Gudanar da Majalisin Juyayin Shahadar Imam Hassan (A.S.) a Da'irar Bauchi

An Gudanar da Majalisin Juyayin Shahadar Imam Hassan (A.S.) a Da'irar Bauchi

An Gudanar da Majalisin Juyayin Shahadar Imam Hassan (A.S.) a Da'irar Bauchi

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha